Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Halaka Kwamandojin Boko Haram Biyu


Sojin Najeriya.
Sojin Najeriya.

A wasu sabbin farmaki da rundunar "Operation Tura Ta Kai Bango" da ke karkashin rundunar Operation Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram suka kaddamar, hare-haren na kara kassara ‘yan bindigan na Boko Haram.

Dakarun Bataliya ta 121 da Bataliya ta 151 sun yi wani kwanton bauna ga
‘yan ta'addan a tsakanin Vuria da Guja da ke kan hanyar mahadar Bani a
yankin Pulka.

Sanarwar da kakakin sojojin Najeriya Birgediya Janar Mohammed Yerima
ya sanyawa hannu, na cewar wannan kwanton bauna ya yi sanadiyyar halaka
manyan kwamandojin Boko Haram biyu da aka dade ana nema ruwa a jallo
wato Abu Bas da Ibn Habib.

Kwamandojin biyu da aka kashe manyan na hanun daman madugun Boko Haram Abubakar Shekau ne da ke aikace aikacensu cikin dajin Sambisa da aka dade ana tattara bayanan sirri akan su.

Abu Bas babban kwamanda ne da ke zama na'ibi ga Abu Fatima yayin da shi
kuma Ibn Habib shi ke zama babban kwamandan da ke kula da manyan
sansanonin Boko Haram na Njimia da Parisu a cikin dajin sambisa.

A cewar shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattawan Najeriya da ke
wakiltar wannan yanki da ake gumurzu ya nuna gamsuwa bisa yadda baki
dayan kwamandojin sojin suka nuna damuwa da wannan yaki ta yadda baki
dayansu ma suna cikin dazukan ana fafatawa tare da su.

Ndume ya ce muddin wannan kokari ya dore to yana da yakinin kafin
damina ta fadi za a iya kammala yakin mutane su koma yankunansu har
su sami damar yin noma.

Shi ma masanin tsaro a Jami'ar Maiduguri, Dr. Mohammed EL-Nur Dongel na
mai ra'ayin cewa kashe manyan kwamandojin ‘yan ta'addan na iya kashe
kwarin gwiwar mabiyansu da hakan ke zama nasara ga sojoji da gwamnatin
kasa.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne tasirin da hakan zai yi wajen
gaggauta kawo karshen wannan yaki a gaba daya da yanzu ke shiga
shekara 11.

A saurari rahoton cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:

Rundunar Sojin Najeriya Ta Halaka Kwamandojin Boko Haram Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00


Karin bayani akan: Janar Mohammed Yerima​, Boko Haram​,Sojin Najeriya, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG