Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Najeriya Na Iya Zama Kasa Mai Jam'iyya Daya


Jamnar Muhammadu Buhari na APC shugaban Najeriya mai jiran gado

Biyo bayan irin nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya da na jihohi bayan ta lashe zaben shugaban kasa hankalin jama'a ya koma akan yiwuwar kasar ta kasance mai jam'iyya daya.

Bayan zabukan da aka gudanar yanzu APC ta samu kashi sittin na 'yan majalisun jihohi da na tarayya tare da shugaban kasa.

Jama'a sun soma dora ayar tambaya akan ko kasar ta doshi hanyar zama kasa mai jam'iyya daya ke nan.

Dr Ramatu Tijjani Aliyu shugabar mata ta kasa ta jam'iyyar APC tace basu yadda da tururuwar da 'yan PDP suke yi zuwa cikin APC ba saboda yin hakan zai kashe ko ya raunata adawa. Tace jajircewar jam'iyyun adawa ya haifar da APC har ta kawo inda take yau. Su ne suka dinga jawo hankulan mutane akan abubuwan da gwamnati keyi da ba daidai ba. Saboda haka idan kowa ya koma APC wanene zai tsawartawa gwamnatin da jam'yyar zata kafa. Idan bata yi daidai ba wanene zai nuna ya kuma jajirce akan a yi gyara.

Ta kira 'yan PDP su tsaya cikin jam'iyyarsu su jajirce. Su tabbatar lallai alkawuran da APC tayi ta cikasu. Ta haka Najeriya zata kafu, dimokradiya kuma ta dore.

Duk da cewa kashi casa'in cikin dari na 'yan jam'iyyar APC daga PDP suka fita tsohon gwamnan jihar Nasarawa shi ma dan jam'iyyar PDP a da, yanzu jigo a APC, yace tururuwar da a keyi zuwa jam'iyyarsu ba zata sa hankali ya gushe ba. Yace duk mutumin kirki dake cikin PDP ya bar jam'iyyar. Idan annoba ce to ta riga ta kaisu. Yace watakila wata sabuwar jam'iyya ta fito da zata iya adawa da APC amma ba PDP ba.

Ahmed Aliyu Wadada tsohon dan majalisar wakilai a jam'iyyar PDP kuma Baraden Keffi yace shi bai ga dalilin barin PDP ba. Yace duk wanda yake son dimokradiya ta cigaba kamata yayi ya tsaya a jam'iyyar PDP domin APC ta samu adawa mai inganci domin a cigaba. Yace wadanda suka tafi APC yana yi masu fatan alheri.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG