Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Sergio Aguero Zai Yi Ritaya Ne Bayan Samun Matsalar Zuciya?


Sergio Aguero (dama) tare da shugaban Barcelona Joan Laporta ranar Mayu 31, 2021.

Dan shekara 33, Aguero ya fuskanci matsalar numfashi yayin karawar da suka yi da Alaves a gasar La Liga.

Dan wasan Barcelona Sergio Aguero zai bayyana matsayar kan makomarsa a fagen wasan kwallon kafa saboda larurar zuciya da ya samu.

A ranar Laraba ake fatan Aguero wanda dan asalin kasar Argentina ne zai bayyana wannan matsaya.

Minti 41 da fara wasan Barcelona da Alaves a gasar La Liga ta kasar Sifaniya a Camp Nou inda suka tashi da da ci 1-1, ake ta yamadidin cewa dan wasan zai jingine takalamsa a fagen tamola.

Dan shekara 33, Aguero ya fuskanci matsalar numfashi yayin wasan, lamarin da ya sa ya fadi rike da kirjinsa kafin daga bisani ya fice daga wasan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Sau biyu aka fara wasa da Aguero cikin wasanni biyar da ya bugawa Barcelona, inda ya zura kwallo daya.

A lokacin bazarar da ta wuce dan wasan ya koma Barcelona daga Manchester City a matsayin dan wasa mai cin gashin kansa.

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG