Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Murkushe 'Yan Ta'ada a Konduga da Bama


Sojojin Najeriya ayankin Bama
Sojojin Najeriya ayankin Bama

Tun daga Maiduguri zuwa Konduga jar Bama sojojin Najeriya ne suke rike da yankin yayin da sojojin sama ke shawagi da jiragen yaki a wuraren.

Sojojin Najeriya sun tabbatar da mallakar garuruwan da ada suke karkashin ikon 'yan Boko Haram.

A garin Bama dai babu kowa tamkar ya zama kufai. Babu abun da ake gani sai baraguzen gidaje da kuma marayu da mata da dattawa.

Kwamandan yaki da ta'adanci a arewa maso gabas Manjo Janar Yusuf Abubakar wanda ya mayarda fadar shehun Bama sansanin sojoji na wucin gadi yace sun tare garin ne domin su nunawa ministan yada labarai irin barnar da aka yi a garin na Bama. A cewar kwamandan babu wani gini dake tsaye a garin.

Tare dasu akwai mataimakin gwamnan Borno domin su ga abun da ya faru su kuma san irin taimakon da zasu yi. Yakamata gyara masu muhallansu.

Akan kawo karshen 'yan ta'adan a wannan watan kwamandan yace suna kokari kuma da yaddar Allah zasu cimma burinsu.

Ministan labarai Lai Muhammed ya nesanta addinin musulunci da 'yan ta'adan duk da cewa kowane gini sun rubuta mashi kalmar shahada. Yace 'yan ta'ada ne kawai da gwamnatin Buhari zata murkushesu.

Shaikh Abdullahi Bala Lau yace masu aikata irin aikin 'yan Boko Haram ba musulmi ba ne domin bata yiwuwa musulmi ya dauki bam ya shiga masallaci ya kashe musallata. Musulmai 'yanuwan juna ne to yaya za'a yi mutum ya dauki bam ko wuka ya shiga masallaci ya kashe musulmi ya kuma ji dadi. A cewarsa wadansu ne suka sanya rigar musulunci su cutar da musulunci da musulmai.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG