Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Wadanne Irin Mutane ne Buhari Zai Nada Ministoci


Shugaba Muhammad Buhari

A daidai lokacin da shugaban Najeriya ya baiwa 'yan kasar tabbacin cewa a wannan watan zai nada ministocinsa tuni kafofin yada labarai suka fara fitowa da sunayen mutanen da suke ganin sun dace.

Wadanda kafofin yada labarai suka fitar da sunayensu suna cewa fitattu ne a wasu bangarori na ayyukan Najeriya, walau daga ayyukan lauya ko na makarantu ko jami'o'i ko kuma ayyuka da suka shafi gwamnati da bangaren diflomasiya.

Irin wadannan ne ake ganin suna kan gaba gaba a cikin mutanen da shugaba Buhari zai zakulo ya nada su ministocinsa.

To amma wasu 'yan kungiyar matasa masu goyon bayan Muhammad Buharin wato Malam Muhammad Sani Riko da Alhaji Kabiru Bala sun ce a yanzu dai duk wani harsashe da mutane ke yi shati fadi ne kawai.

Amma tilas mutanen da zai zaba su kasance mutane da suka shahara wurin kyamar cin hanci da rashawa da kuma rikon amana wurin gudanar da ayyukansu na gwamnati ko kuma bangare na kasuwancinsu.

Alhaji Kabiru Bala yace furucin da ya fito daga bakin shugaban bai fayyace ko gogaggun ma'aikatan gwamnati ko jami'o'i ba ne zai zakulo. Abun da yace shi ne zai zabi masana masu ilimi wadanda zasu iya yin aikin da ya dace da abun da yake son ya sanyasu su yi.

Na farko yana son ya yi aiki da wadanda zasu ceto tattalin arzikin kasar. Dole yana bukatar masana kan wannan bangaren. Ya kuma fada yana son ya nada wadanda basu da wani kashi a gindinsu. Yana bukatar wadanda zasu yi aikin da zai bashi kwanciyar hankali..

Saidai a yanayin da Najeriya ke ciki samun mutanen da basu da kashi a gindinsu zai yi wuya.

Shi ko Muhammad Riko yace a kwai hujja lallai mutane su yadda shugaba Buhari zai kawo mutanen da zasu rike amana. Amma yace dole a yi hattara domin kada a kawo wasu mutane saboda bangaranci ko kuma domin suna kusa dashi ko kuma saboda son zuciya.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG