Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Ta Tallafawa Manoma A Najeriya A Wani Sabon Shirin Noma Da Cinikayyar Amfanin Gona


Mahallarta taron FCDA
Mahallarta taron FCDA

Ofishin raya kasashe na kasar Burtaniya ta bullo da sabon Shirin bunkasa harkokin noma da cinikayyar amfanin gona, domin tallafawa kananan manoma a wasu jihohin Najeriya, cikin har da jihar Jigawa.

Gwamnatin Burtaniya karkashin ofishin raya kasashe na kasar ta bullo da sabon Shirin bunkasa harkokin noma da cinikayyar amfanin gona, domin tallafawa kananan manoma a wasu jihohin Najeriya, cikin har da jihar Jigawa. Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da manoman jihar ke kokawa kan rashin samun daidaito wajen tsare tsaren bunkasa noma na gwamnatin jihar.

Jimlar fam milyan 95 ne gwamnatin ta Burtaniya ta kebe karkashin sabon Shirin da ta yiwa lakabi Propcom+ wadda zai maida hankali akan karfafa tattalin arzikin kananan manoma da sha’anin sauyin yanayi da sauran al’amura masu nasaba da noman zamani.

A ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa, Dr Adiya Ode Jami’a daga ofishin hukumar FDCO a Najeriya ta ce Shirin Propcom+ wadda zai dauki tsawon shekaru 8 ana aiwatar dashi a wasu jihohin Najeriya na fatan yalwata arzikin kananan manoma miliyan 4 kuma 40% zasu kasance mata ne.

Jigawa dai na cikin jihohin da sauyin yanayi ke mummunan tasiri ga manoman su, a cewar Hajiya Aisha Ibrahim Hadejia, guda cikin manoma mata a jihar. “Sauyin yanayi ba karamar matsala ba ce game da rayuwar Manoma, saboda idan ambaliya ta wakana tana hana samun amfani mai yawa”

Shirin tallafi ga manoma na hukumar FCDO na zuwa ne a dai dai lokacin da manoman a Jigawa ke korafi akan fasalin rabon kayan tallafa musu a jihar. Malam Mansur Salisu Auyo da Habibu Manzo Babura na cewa, “Idan dai tallafi ne na gwamnati, mafi yawanci lokuta, ‘yan siyasa ne ke amfani da sunayen mutane suke turawa ake basu, amma ba manoman daya dace a basu ba”

Sai dai Hajiya Aishatu Ibrahim Hadejia ta ce irin shukawa mai yi da wuri kuma wadda yake dauke da sinadaran gina jiki, musamman ga kananan yara na kadan daga cikin abubuwan da suke sa ran samu dag hukumar FCDO a karkashirinta na Propcom+.

A cikin watan gobe na Janairu ne ake sa ran Shirin na Propcom+ zai fara aiki gadan gadan a jihohin Jigawa da Kano, Kaduna, Adamawa, Borno da kuma Yobe, kuma shekaru ukun farkon aiwatar da Shirin za’a kashe Fam miliyan 55.

FCDO AGRIC NIGERIA.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG