Accessibility links

Shugaba Barack Obama Yace Tilas 'Yan Majalisa Na Jam'iyyu Su Gaggauta Cimma Matsaya


Shugaba Barack Obama na Amurka yana magana Jumma'a 29 Yuli 2011 kan daurin gwarmai da aka samu game da batun kara yawan bashin da doka ta kyale cewa za a iya bin gwamnati

Idan ba a daidaita kan batun kara dokar yawan bashin da gwamnatin Amurka zata iya karba nan da talata ba, Amurka zata kasa biyan bukatunta na kudi

Shugaban Amurka Barack Obama, yace ana kara fuskantar matsin lamba da kuma kurewar lokaci ga 'yan Democrat da Republican dake majalisar dokoki su cimma daidaito a kan matakin kara yawan bashin da gwamnati zata iya karba da kuma rage kudaden da ta ke kashewa.

Mr. Obama yace sassan biyyu sun yarda da juna a kan yawan kudaden da ya kamata a rage daga abinda hgwamnati ke kashewa, da kuma yadda za a gyara tsarin saka haraji da rage kudaden tallafawa rayuwar yau da kullum ta jama'a.

Shugaban 'Yan Democrat Masu Rinjaye A Majalisar dattijai, Harry Reid
Shugaban 'Yan Democrat Masu Rinjaye A Majalisar dattijai, Harry Reid

Yace shugaban 'yan Democrat a majalisar dattijai ya gabatar da shirin da sassan biyu zasu iya zama su sasanta a kai, yana mai fadin cewa shi ma shugaban 'yan Republican a majalisar dattijan ya gabatar da shawarwari masu ma'ana. Ya soki lamirin 'yan Republican na majalisar wakilan tarayya a saboda ci gaba da suke yi da kokarin zartas da shirin da ya ce ba zai taba zamowa doka a kasar nan ba.

Shugaban ‘yan Democrat masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka, Harry Reid, yace zai nemi a jefa kuri’a yau jumma’a a kan shirinsa na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da dala miliyan sau miliyan biyu da dubu dari hudu, yayin da zai kara adadin kudaden da gwamnati zata iya karba bashi da yawan da zai sa gwamnatin ba zata saker bukatar yin hakan ba har zuwa karshen shekarar 2012.

Kakakin majalisar wakilan tarayya dan jam'iyyar Republican, John Boehner
Kakakin majalisar wakilan tarayya dan jam'iyyar Republican, John Boehner

A daidai wannan lokaci kuma, ‘yan jam’iyyar Republican dake jagorancin majalisar wakilan tarayya ta nan Amurka su na ganawa a yau jumma’a domin sake fasalin shirinsu na kara adadin kudin da gwamnati zata iya karba bashi tare da zabtare kudaden da ta ke kashewa, kwanaki hudu kacal kafin gwamnatin ta Amurka ta fuskanci yiwuwar kasa iya biyan bukatunta na kudi.

Ala tilas a jiya alhamis, ‘yan Republican sun jinkirta jefa kuri’a a kan shirin da kakakin majalisar John Beohner ya zana wanda zai kara yawan adadin dala miliyan sau miliyan 14 da dubu 300 da ake iya bin gwamnatin Amurka bashi a yanzu, yayin da zai nemi zabtare dala miliyan dubu 900 daga abinda gwamnatin ta ke kashewa a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Boehner bai samu kuri’un da yake bukata don zartas da wannan shirin daga ‘yan’uwansa ‘yan Republican ba, yayin da shugabannin jam’iyyar Democrat a majalisa suka ce dukkan ‘ya’yansu baki daya su na adawa da wannan shirin. Wasu ‘yan Republican, ciki harda ‘yan bangaren nan na masu matsanancin ra’ayin rikau da ake kira Tea Party, su na yin adawa da shirin na Boehner a saboda ba zai zabtare kudaden da gwamnati ta ke kashewa kamar yadda suka so ba.

XS
SM
MD
LG