Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bashir Na Sudan Ya Ki Janye Dakarunsa Daga Abyei


Yankin Abyei na Sudan kenan ke cin wuta

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya ce arewacin Sudan ba zai janye daga yankin Abyei da ake takaddama a kai ba, wanda dakarunsa su ka mamaye kwanan nan.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya ce arewacin Sudan ba zai janye daga yankin Abyei da ake takaddama a kai ba, wanda dakarunsa su ka mamaye kwanan nan.

Shugaba Bashir ya fadi a wani jawabinsa a jiya Talata cewa yankin Abyei na arewacin Sudan ne. Y ace ya kuma bayar da umurni ga dakarun arewa su mayar da martani ga duk wata takala daga sojojin kudu.

A makon jiya ne sojojin arewacin Sudan suka kutsa cikin yanki mai arzikin man fetur din, wanda da arewa da kudu wanda ke dab da samin yancin kai ke ikirarin nasa ne.

Da safiyar jiya Talata, wani Minista dan asalin kudancin Sudan ya yi murabus daga gwamnatin kasar, yana mai zargin arewa da aikata laifin yaki. Luka Biong Deng, Ministan Harkokin Ma’aikatun Gwamnati, ya ce a yanzu fa ba zai iya cigaba kasancewa a gwamnatin hadin gwiwa da jam’iyya mai mulki ta arewacin kasar ba.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, ta gaya wa manema labarai a babban birnin Kudancin Sudan a jiya Talata cewa an sami munanan rahotannin wasoso da kone-kone a Abyei tun bayan da sojojin arewa su ka mamaye yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 15,000 ne su ka tsere zuwa kudu don guje wa fada a Abyei.

XS
SM
MD
LG