Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sabbin Fashe-fashe Sun Girgiza Birnin Trabulus


Yadda NATO ke barin wuta kan cibiyoyin gwamnatin Gaddafi.

Fashe-fashe da dama sun girgiza, Trabulus, babban birnin Libiya da asubar yau Jumma’a. Zuwa yanzu ba a sami rahotannin wadanda abin ya rutsa das u ba.

Fashe-fashe da dama sun girgiza, Trabulus, babban birnin Libiya da asubar yau Jumma’a. Zuwa yanzu ba a sami rahotannin wadanda abin ya rutsa das u ba.

Cikin jerin daren da su ka gaba, NATO ta yi ta jefa bama bamai kan wasu wurare a Trabulus, ciki hard a katafaren gidan Shugaba Muammar Gaddafi inda yak e kuma bayar da umurni ga sojojinsa. Tun bayan da wani harin NATO ya hallaka wani dan Gaddafi cikin watan Afrilu, ba a cika ganin sa a bainar jama’a ba.

A halin da ake ciki kuma, wata ‘yar kasar Libiya da ta yi zargin cewa sojojin Gaddafi sun mata fyade, an tasa keyarta karfi da yaji daga kasar Qatar zuwa Birnin Benghazi na gabashi da ke karkashin ikon ‘yan tawaye.

Jami’an hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya sun ce matar mai suna Imad al-Obeidi na jiran a sake tsugunar da ita kuma hukumar na kan shirya takardun dauketa daga Qatar zuwa wata kasa ta uku a lokacin. Jami’an sun ce tasa keyar al-Obeidi da aka yi ya saba wa dokar kasa da kasa.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner y ace Amurka ta damu da lafiyar al-Obeidi kuma ta yi ta kokarin ganin ta sami irin mafakar da ta dace. Toner y ace jami’an gwamnatin Amurka sun zanta da ita kwanan nan.

Al-Obeidi ta abka cikin wani otel a Trabulus cikin watan Maris, inda ta gaya wa jan jaridar kasashen waje cewa dakarun gwamnatin Libiya sun yi mata fyade, wai sun yi fakonta ne don sun ga daga Benghazi ta fito. To saidai ba a iya tantance zargin yi mata fyaden ba daga wata kafa dabam.

Hukumomin Libiya dai sun yi ta bayyana ta da cewa ‘yar giya ce, ko kuma karuwa ko barauniya.

XS
SM
MD
LG