Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bazoum Mohamed Zai Kai Ziyara Jihar Maradi


Shugaban Nijar Bazoum Mohamed

A ci gaba da zagayen al’umomin yankunan dake fama da matsalar tsaro Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum zai ziyarci jihar Maradi a ranakun 1 da  2 ga watan Agusta, wata guda kenan bayan rangadin da ya gudanar a jihar Diffa yankin da dubban ‘yan  gudun hijira suka fara komawa garuruwansu na asali.

Jihar Maradi na daga cikin yankunan da suka tsinci kansu cikin tashin hankali inda masu satar shanu da masu garkuwa da mutane suka addabi jama’a bayan tabarbarewar al’amuran tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka hada da Katsina, Zamfara da Sokoto.

Dubban ‘yan Najeriya ne suka tsallaka zuwa wasu sassan jihar ta Maradi yayin da wannan matsala ta tilastawa wasu ‘yan jihar kaura daga matsugunansu domin neman mafaka, abinda ya sa shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum zai yi tattaki zuwa wannan yanki domin jaddadawa talakawa goyon baya tare da ba su tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen wannan matsala da ta ki karewa ba.

Gwamnan Maradi Zakari Oumarou ya kira wani taro domin sanar da al’uma makasudun wannan ziyara ta shugaban kasar.

Mazaunan jihar ta Maradi sun yi murna da jin wannan labari ganin yadda ayyukan ‘yan bindiga suka haifar da koma bayan harakokinsu na yau da kullum.

Jihar Maradi wacce ke matsayin yanki na biyu mafi yawan al’uma a Jamhuriyar Nijar bayan jihar Damagaram ita ce jihar da ake dauka a matsayin cibiyar kasuwanci ta kasar baki daya inda a kowace rana hada-hada ke kara karfafa a tsakanin ‘yan kasuwar Nijar da na Najeriya.

La’akkari da wannan ya sa kasashen biyu za su shimfida layin dogo daga jihar Kano a Najeriya zuwa Maradi saboda haka batun farfado da kasuwanci na daga cikn batutuwan da shugaban kasa zai tattauna akan su da mutanen Maradi a yayin wannan ziyara ta awoyi 48 kafin ya daga zuwa Damagaram inda za a yi bikin ranar samun ‘yancin kai ta 3 ga watan Agusta.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Shugaba Bazoum Mohamed Zai Kai Ziyara Jihar Maradi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00


Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG