Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Je Kano Bikin Cika Shekaru 58 Da Kafuwar Rundunar Sojan Saman Najeriya


Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya na daukar matakan da suka dace domin wadata rundunar sojojin saman Najeriya da kayayyakin aiki na zamani, inda ya bukaci jami’an rundunar su kara kaimi wajen murkushe ayyukan ta’addanci a sassan kasar.

Shugaban Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin a jihar Kano, a yayin bikin cikar rundunar shekara 58 da kafuwa.

Majalisar dokoki ta kasa ce ta amince da kudirin dokar kafa rundunar sojojin sama ta Najeriya a shekarar 1962, bayan da hukumomin kasar suka fahimci bukatar samar da rundunar.

Hakan ya biyo bayan fafatawa da sojojin Najeriya suka yi a aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen Congo da Tanzania a shekarar 1961, inda aka yi amfanin da jiragen sojojin sama na ketare wajen jigilar dakarun Najeriya zuwa fagen daga da kuma dawo da su gida.

Sai dai a hukumance rundunar sojin sama ta Najeriya ta fara aiki ne a shekarar 1964, bayan daukar jami’ai da kuma basu horon da ya kamata.

A yau ne dai rundunar ke cika shekaru 58 da kafuwa, inda ake bukukuwa na musamman da kuma gabatar da jawabai a Kano, a taron shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da bada kulawar da ta kamata ga rundunar.

“Mun amince a sayo karin kayayyakin aiki ga rundunar sojojin sama domin jami’anta su kula da sararin samaniyar mu yadda ya kamata. A matsayin mu na gwamnati ina bada tabbacin cewa, zamu ci gaba da tallafa wa rundunar da jami’anta tare da karfafa musu gwiwa domin magance kalubalen tsaro da mu ke fuskanta,” a cewarsa.

Gabanin halartar taron da ya wakana a filin taro na shalkwatar rundunar sojojin sama da ke daura da tashar sauka da tashin jiragen sama ta Aminu Kano, shugaba Buhari ya ziryarci mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa. Mai martaban ya godewa shugaba Buhari tare da jinjina masa saboda ayyukan alheri da ake yi a jihar da kasar baki daya.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mukarraban gwamnatinsa ne su ka tarbi shugaban a yayin ziyarar tare da yi ma rakiya bayan kammala ta.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG