Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yi Marhabin Da Shirin Kafa Cibiyar Raya Afurka Ta Kamfanin Microsoft Kan Dala Miliyan 200


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a Abuja, ya ce Najeriya a shirye ta ke ta yi maraba da karin kudirori da saka hannun jari kan fasahar lataroni, yayin da ya yaba shirin kafa Cibiyar Raya Afurka ta Microsoft, da za ta ci dala miliyan 200.

Da yake karbar bakuncin shugaban Sashin Kasuwanci na kamfanin na Microsoft, Brad Smith, a fadar gwamnati tare da rakiyar Ministan Sadarwa da Tattalin arziki da Fasahar Dijital, Farfesa Isa Ali Pantami, shugaban ya ce: “An sanar da ni cewa Cibiyar Raya Afurka a Najeriya za ta zama cibiyar injiniya ta farko ta Microsoft a Afurka wadda za a kafa kan kudi miliyan 200.

"An kuma sanar da ni shirin fasaha na Microsoft wanda ke da nufin horar da 'yan kasa miliyan biyar da samar da ayyukan yi 27,000 a cikin shekaru uku masu zuwa. Wadannan tsare-tsare abin yabawa ne kuma ina rokon ku da ku fadada su kuma ku ci gaba da ba Najeriya fifiko yayin da kuke aiwatar da ayyukanku na kasa da kasa.’’

Shugaba Buhari ya shaida wa tawagar ta Microsoft da ta ziyarci kasar cewa, a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan al'umma a Afurka, an sanya Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a tsarin fasahar zamani na kasa da kasa tare da neman hadin gwiwa don amfani da abubuwan da za a iya samu.

Ya ce daya daga cikin irin wadannan muhimman ayyukan hadin gwiwa shi ne a fannin inganta iya aiki.

Baya ga hadin gwiwa a fannin inganta sana’o’i, shugaba Buhari ya ce yana fatan kara hadin gwiwa da zai tallafa wa tsarin samar da ababen more rayuwa na zamani, dangane da fasahohin da ke tasowa.

"Na yi imani zai kasance da amfani sosai kuma cin moriya ga Microsoft da Najeriya idan aka fadada aikin haɗin gwiwar a fiye da wurare huɗu da ake da su a yanzu a wannan ƙasa.

Shugaban tawagar ta Microsoft kuma Mataimakin Shugaban Kamfanin ya ce kamfanin zai ci gaba da samar da ayyukan yi don taimakawa wajen gina fasahar da za ta canza duniya.

"Mun yi alkawarin horar da mutane miliyan biyar a Najeriya nan gaba," in ji Smith, yana mai cewa "mutane 60,000 sun riga sun shiga kwasa-kwasai yayin da 300,000 suka kammala kwasa-kwasai daban-daban."

Shugaban na tawagar ta Microsoft ya ce kamfanin ya yi hadin gwiwa da wasu kamfanoni don kara yawan Intanet da na'urorinta.

XS
SM
MD
LG