Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Ziyarci Wadanda Harin Bamabamai Ya Raunata


Shugaba Muhammadu Buhari

Jiya Lahadi shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai ziyara asibitin kasa ko National Hospital inda ya gayar da wadanda harin bamabamn Kuje da Nyanya ya raunata.

Shugaba Buhari ya yiwa wadanda harin ya rutsa dasu fatan alehi da samun sauki da wuri.

Shugaban ya tabbatar masu cewa gwamnatin tarayya zata dauki nauyin biyan kudaden jiyyarsu.

Kazalika shugaban ya umurci shugaban ma'aikatan fadarsa Malam Abba Kyari da ya biya N268,790.00 kudin jinyar wata yarinya dake kwance a sashen yara.

Uwar yarinyar Deborah Stephen ta fashe da kuka da ta ga Shugaba Buhari. Ta fada masa 'yan fashi da makami ne suka harbi yarta yayinda suka shiga gidansu. Tace basu da kudin biyan asibitin.

Shugaban da ya ziyarci asibitin tare da wasu ma'aikatansa ya samu rakiyar gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun. Tare suka ziyarci sashen wadanda ke samun kulawar gaggawa da na yara da kuma sashen kowa da kowa.

Yayinda yake mika godiyarsa saboda ziyarar, shugaban asibitin Dr Jafaru Momoh yace zuwan shugaban zai taimaka wurin gaggauta warkewar masu jinyar. Yace zasu dauki ziyarar shugaban a matsayin karramasu da nuna masu kauna da kuma basu tabbacin cewa kasar gaba daya tana sane da halin da suke ciki ta kuma nuna masu kauna da kulawa.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG