Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Dan Takarar Gwamnan Zamfara


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

‘Yan bindiga da ba a iya tantance iya adadinsu ba sun koma tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka afka wa matafiya tare da harbe wani tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara, Alhaji Sagiru Hamidu, tare da sace wasu da dama.

Wani mutum da ya tsira da ranshi a harin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce 'yan bindigar sun bude wuta ne kan matafiya don tsaida su lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar tsohon dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sagiru Hamidu, da wani mutum daya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe hudu na yammacin ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da matafiya da dama.

Faifan gidiyo da ke yawo a kafaffen sada zumunta na Instagram ya nuna motoci a tsakiyar titi ba mutane, da gawar wani mutum ciki babbar riga inda daga bisani ‘yan sanda suka iso wurin da lamarin ya faru.

An ga jami’an ‘yan sanda cikin motarsu a yayin da su ke sahun gaba don bude hanyar ga matafiya da suka tsaya domin gudun abin da ka je ya dawo a wani faifan bidiyo a kafar sada zumunta na Instagram.

Rahotanni sun yi nuni da cewa maharan sun tare titin daura da kauyen Rijana da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja suka aikata ta’asar.

A cikin faifan bidiyon, wasu mutane 3 da suka tsira da ransu sun ce ‘yan bindigar sun yi amfani da damar lalacewar da hanyar ta yi da kuma tattare wurare don gyara suka aikata wannan danyen aikin.

Lalacewar wasu bangarorin hanyar Kaduna zuwa Abuja na tilastawa matafiya a motoci tafiya kan hanzkali kuma a kan hannun titin daya da ke cike da hatsarin gaske baya ga matsalar dauke mutane da yan bindigar suka yi.

Rahotanni daga kauyuka makwabta da Rijana sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar ne daf da kauyen ne tun da misalin karfe uku na rana inda suka ci karensu ba bu babbaka, ba tare da wata turjiya ba a tsawon sama da sa’a daya.

Duk da cewa an ga wasu ‘yan sanda a cikin motar aikinsu kirar Hilux na kokarin bude hanyar a wani faifan bidiyo, har y yanzu dai rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ba ta tabbatar ko karyata lamarin ba.

An kwashe wasu tsawon lokaci yan bindigar ba su tare hanyar ta Kaduna zuwa Abuja ba sakamakon karfafa matakan tsaro da gwamnati ta dauka a baya.

Masana tsaro dai na alakana dawowar yan bindigar kan titin Kaduna zuwa Abuja da rufe layin salula a wasu bangarorin jihar Kaduna da kuma yajin aikin ma’aikatan hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya da ya tilastawa matafiya bin hanya.

XS
SM
MD
LG