Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump zai jagoranci Amurkawa tunawa da hare haren ranar sha daya ga watan Satumban shekarara 2001


Ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya
Ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya

Shugaba Donald Trump a karon farko a matsayinsa na shugaban kasa zai jagoranci Amurkawa a yau Litinin wurin tunawa da hare haren ranar sha daya ga watan Satumban da aka kaiwa New York da Washington a shekarara 2001

Trump zai yi bukin cika shekaru 16 na tuna aikin ta’addanci mafi muni a kasar Amurka a fadarsa ta White House, kana ayi tsit na lokaci kalilan a daidai karfe takwas da minti arba’in, daidai lokacin da jirgin farko da yan ta’addan al-Qaida da suka yi fashinsa abkawa cibiyar kasuwanci ta duniya a birnin New York.

Wani jirgi na biyu ya sake abkawa benen na cibiyar kasuwancin duniyar bayan minituna 23 kana wannan makeken bene ya rushe da wuta daga bisani hayaki ya turnuke wurin.

Baya ga haka kuma, Trump zai halarci bukin tuna wannan ranar a yau Litinin a ma’aikatar tsaro ta Pentagon da aka kai hari, kuma aka mata mummunar barna yayin da jirgin fasinja daya daga cikin jirage hudu da yan ta’addan suka yi fashinsa a wannan rana. Da safiyar yau Litinin an sauke tutar Amurka a gefen ginin.

Mataimakin shugaba kasa Mike Pence zai je Shanksville a jihar Pensylvania inda wani jirgin da shima aka yi fashinsa ya fadi a kan wani fili.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG