Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Joe Biden Ya Yi Wa Dansa Hunter Biden Afuwa


Joe Biden da Dansa
Joe Biden da Dansa

Shugaban Amurka Joe Biden yayi afuwa ga dansa Hunter, yana mai kokarin ceto dan daga hukuncin dauri a gidan yari akan laifukan da suka shafi bindiga da kuma haraji, inda kuma ya yi fatali da alkawuran da ya dauka a baya, na cewa ba zai yi amfani da karfin ikon shugaban kasa domin amfanin gidansa ba.

A can baya shugaban kasar dan jam'iyyar Democrat ya ce ba zai yafe wa dansa ko kuma ya sassauta hukuncin da aka yanke masa ba, bayan yanke masa hukunci a shari'o'i biyu a jihohin Delaware da California.

Wannan matakin dai na zuwa ne 'yan makwanni kafin Hunter Biden ya fuskanci hukuncinsa, bayan da aka tabbatar masa da laifi na sha’anin bindiga, da kuma amsa laifi da yayi kan abin da ya shafi haraji, kuma kasa da watanni biyu kafin zababben shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House.

An kwashe dogon lokaci ana shari'ar ta ɗan shugaban kasar, wanda ya fito karara ya bayyana cewa ya fuskanci binciken gwamnatin tarayya a watan Disamban shekara ta 2020, wata guda bayan nasarar Joe Biden a shekarar ta 2020.

A watan Yuni ne Biden ya yanke shawarar cewa ba zai yi wa dansa afuwa ba, inda ya fada wa manema labarai cewa dansa na fuskantar shari'a akan bindiga a Delaware, ya ce "Zan amince da hukuncin da masu taya alkali yanke hukunci suka yanke. Ya kara da cewa zan yi hakan kuma ba zan yi masa afuwa ba.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG