Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Joe Biden Zai Tattana Da Sanatocin Jam'iyyar Republican Kan COVID-19


Shugaba Joe Biden
Shugaba Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden na shirin karbar bakuncin wasu sanatoci 10 ‘yan jam’iyyar Republican don tattaunawa yau Litinin game da wani sabon zagaye tallafin tattalin arzikin coronavirus.

Taron na Fadar ta White House ya zo ne bayan da ‘yan Jam’iyyar ta Republican suka aika wa Biden wasika, suna bukatar sa a ranar Lahadi da ya tattauna kan kudirin da ya gabatar na dala tiriliyan 1.9 maimakon kokarin ganin an amince da shi kawai da kuri’un‘ yan majalisar dokoki ta Democrats.

'Yan Republican sun nemi karamin zagaye na tallafi, gami da tsaurara matakai kan wadanda za su cancanci a basu kudin kai tsaye.

A cikin yarjejeniyar ta hadin kai ba tare da banbancin siyasa ba, sanatocin na Republican sun rubuta cewa, “mun kirkiro wani tsari na tallafin COVID-19 wanda ke ginawa a kan dokokin taimako na farko na COVID, dukkansu sun sami amincewa da goyon bayan bangarorin biyu, "Shawarwarinmu sun nuna yawancin abubuwan da kuka bayyana masu mahumminci, kuma tare da goyon bayanku, mun yi imanin cewa Majalisar za ta iya amincewa da wannan shirin da sauri tare da goyon bayan bangarorin biyu."

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG