Accessibility links

Shugaba Jonathan ya ce Gwamnatinsa ta Samu Nasara a Shekarar 2013


Shugaba Goodluck Jonathan

A wani jawabi da ya rubuta kuma ya rabawa kafofin labarai shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ta samu nasara a shekarar 2013

A Najeriya jiya ne shugaba Goodluck Jonathan ya bada wani jawabi na musamman a rubuce inda ya yi ikirarin gwamnatinsa ta samu nasara a shekarar 2013 da ta shude.

Jawabin na musamman ya rabawa kafofin labarai wanda ya ambato cikawa shekara dari da kafa kasar Najeriya. A cikin jawabin ya yiwa 'yan kasar albishir a kan irin ayyukan da zai yai domin inganta rayuwarsau da tabbatar da cewa an samu cin moriya irin na dimokradiya.

A cikin jawabin ya bayyanawa 'yan kasa cewa shi kan ya ga gwamnatinsa ta ci nasar a shekara ta 2013 ganin irin nasarorin da ta samu wurin bada yanayi mai kyau da kasa da kasa aka amince cewa Najeriya ita ce cibiya mai kyau da za'a iya saka jari a ciki. Ya cigaba da cewa an samu nasarori masu yawa wurin samarda madatsun ruwa wadanda zasu kawo yalwatuwa na albarkatun kasa musamman yin noman rani da samun ruwan sha. Ya bayyana irin nasarar da a ka samu a makarantu da ingantasu a cikin kasar da gina wasu sabbi. Ya ce an tabbatar an yaki cin hanci da karbar rashawa musamman a bangaren sha'anin da ya shafi samarda takin zamani ta yin anfani da wayar hannu. Ya ce wannan ya baiwa Najeriya nasara domin manoma sun samu takin zamani ba tare da fuskantar irin matsalolin da ba.

Da yake nuna irin matakan da zai dauka domin tabbatar da cewa gwamnatinsa ta yaki barnatar da kudade ya ce lalle an fito da wasu tsare-tsare da za'a yi anfani da naurori masu kwalkwalwa domin like duk wata kafa da kudade ke bi su salwanta. Ya ce akwai tabbataccen alkawari da zai yiwa 'yan Najeriya cewa lallai a wannan shekarar za'a rage tafiye-tafiye da yawan jami'an gwamnati ke yi da irin dimbin kudin da gwamnati ke kashewa. Za'a rage tafiya kasashen ketare kama daga ofishinsa har zuwa sauran manyan kusoshin gwamnati.

Wasu kwararru a kan sha'anin zamantakewa irin su Dr. Kabiru Abdulkadir 'Yarmama wanda shi ne sakataren kungiyar sa kai ta kasa da kasa dake kula da harkokin kare muhalli da makamashi tare da Malam Mohammed Bunu Ahmad kwararre kan bunkasa makamashi da harkokin mai a Najeriya. Dr 'Yarmama ya ce shugaban ya yi jawabi to amma abun da ya fada suna nan a kasa da za'a gani a kuma tabbatar dasu? Idan aka dauki harakar ilimi misali da mutane daga wasu kasashe suna zuwa yin karatu a Najeriya domin ingantacce ne . Amma yanzu suna zuwa? Hukumar Dinkin Duniya UNESCO ta gwada jami'o'in Najeriya babu daya dake cikin 1000 na farko a duniya. Idan da gaske an inganta ilimi to ai yakamata a gani. Yajin aikin da malaman jami'a suka yi na 'yan watanni biyar da 'yan kai ya yi daidai da hurucin da shugaban kasa ya yi? Shi kuma Malam Ahmad ya ce jawabin shugaban kasa ra'ayi ne nasa, da shi da jami'ansa. Saura 'yan kasa su auna su fadi zahirin menen ke kasa. Yau babban abun da ya damu dan Najeriya shi ne zaman lafiya wanda babu shi . Idan an je ofisoshin gwamnati duk an keresu domin tsoron kada akai masu hari.

Umar Faruk Musa nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG