Accessibility links

Sanadiyar mugun harin da 'yan ta'ada suka kan Nyanya shugaba Jonathan ya kira taron gaggawa da manyan jami'ansa.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kira wani taron gaggawa da manya-manyan jami'an shi na tsaro bayan munanan hare-hare da kuma sace 'yanmata 'yan makaranta fiye da dari.

Haka kuma ya gana da wasu gwamnonin jahohin kasar ajiya Alhamis. Sai dai ban da gwamnonin jam'iyar APC ta adawa , ko da yake wasun su na wakiltar yankunan da suka fi fama da bala'in tashin hankalin da ke faruwa a kasar.

Amma duk da rashin zuwan gwamnonin na jam'iyar APC, gwamnan jahar Akwa Ibom Godswill Akpabio ya shaidawa manema labarai cewa dole ne duka 'yan kasar Najeriya su hada kai su, su warware wannan matsala.

Mr Akpabio yace "dole mu fuskanci al'amarin kuma abu ne da bai kamata a soka siyasa a ciki ba. Bai kamata mu kawo siyasa cikin batun tsaro ba. Ana bukata taimakon kowa da kowa. Kasar baki daya. Dole ne kowane dan Najeriya ya bayar da gudunmowar sa don a ga baya wannan al'amari."

Gwamnan na Akwa Ibom ya ci gaba da cewa "wannan tashin hankali ya na zama kamar kwayar HIV mai haddasa cutar AIDS. Idan bai taba ka kai tsaye ba, ya taba wanin ka."

Gwamnan na jahar Akwa Ibom Godswill Akpabio yace ranar Laraba mai zuwa shugaba Jonathan zai kira wani taro na biyu wanda zai hada da gwamnonin jam'iyar adawa.

A wannan mako wasu jerin hare-hare sun girgiza Najeriya a ciki har da tashin boma-boman ranar Litinin da suka halaka mutane 75 a kalla a Abuja.

Haka kuma a ranar ta Litinin wasu 'yan bindigar da ba a tantance ko su waye ba sun kai hari kan wata makarantar sakandare a jahar Borno suka sace dalibai fiye da dari.

Babu ikirarin daukan alhakin sace daliban, amma harin yayi kama da hare-haren da kungiyor 'yan tsageran Boko Haram ke kaiwa.

Ranar Laraba cibiyar yada labaran sojojin hadin guiwar Najeriya ta ce an kubutar da akasarin 'yan matan, amma shugaban makarantar ya musanta labarin.
XS
SM
MD
LG