Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Na Cin Karensu ba Babbaka a Jihar Borno


Hafsan hafsoshin hafsin tsaron kasa, Air Marshal Alex Badeh
Hafsan hafsoshin hafsin tsaron kasa, Air Marshal Alex Badeh

Jihohin Adamawa da Yobe da Borno suke cikin dokar ta baci domin aika-aikar kungiyar Boko Haram to amma jihar Borno ita ce ta fi samun yawan hare-hare daga kungiyar. A kowane lokaci a ko ina kuma 'yan kungiyar su kan kai hari ba tare da an kamasu ba

Kungiyar Boko Haram ta fi kai yawan hare-hare a jihar Borno ba tare da an samu a kama 'yan kungiyar ba. Harin baya bayan nan har ya kaiga sace dalibai mata daga makarantarsu dake garin Chibok.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yace dokar ta baci da aka kafa bata haifi da mai ido ba a jihar Borno inda hare-hare sai karuwa su keyi. A cikin jihohi ukun dake karkashin dokar ta baci a jihar Borno kadai mahara ke cin karensu ba babbaka. Sai abun da suka ga dama su keyi a kuma lokacin da suke so ba tare da an kama kowa ba kamar yadda suka je makarantar 'yan mata a Chibok suka kwashe yara 247 a cikin motoci har suka yi gaba dasu babu wanda ya tuhumesu ko yace masu uffan.

Sanata Ali Ndume daya daga cikin sanatocin da suka fito daga jihar ta Borno yace abun kunya ne ma ace ba za'a tabbatar da magana ba sai mutane sun fito. Yace babu wanda ya yi masa magana a cikin jami'an tsaro. Yace mutane da basu san abun dake faruwa ba sai su fito suna maganganu.

Wakiliyar Muryar Amurka ta tambayi Sanata Ndume ko akwai wani mataki da yake shirin dauka sai yace su dai sun bar komi a hannun Allah domin babu wanda ya san abun da zai faru. Dalili kwa yace suna fada amma ba'a ji kuma ba'a anfani da abun da suke fada. Yace an maida abun kamar ba na hada kai ba ne domin a kawo karshensa. Yace abu ne kowa sai ya fadi nasa. Abu ne wanda ya kan kaiga gardama da musu har ma ya zama kamar gaba, karya ko sharri. Yace har yanzu gwamnati bata tunkari abun tsakaninta da Allah ba.

Kungiyar 'yan asalin Chibok a Abuja ta shawarci gwamnati da ta tashi tsaye wajen daidaita alamura musamman a jihar Borno. Fogu Bitrus shugaban kungiyar yace suna son gwamnati tayi abun da ya kamata. Yace gwamnati ta je ta kwato 'yan matan da aka sace wato su 247 a mayar dasu wajen iyayensu. Wadanda suka fito su 'yan matan ne da kansu suka yi dabara suka kwaci kansu. Lokacin da aka kai harin mutane kauyen sun kirasu. Lokacin su ma suna waya da mutane yayin da wasunsu na cikin duwatsu. To yanzu mutanen kauyen sun fita da kwari da bakansu suna neman 'ya'yansu.

Ga rahoton Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG