Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya bukaci Masar ta dauki matakin mika mulki


Masu zanga zangar kin jinin shugaba Hosni Mubarak a dandalin 'yanci yau Lahadi.

Jami’an fadar White House sun ce shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shaidawa shugabannin kasashen duniya da dama cewa, tilas ne shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya fara daukar matakin mika mulki cikin sauri yanzu

Jami’an fadar White House sun ce shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shaidawa shugabannin kasashen duniya da dama cewa, tilas ne shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya fara daukar matakin mika mulki cikin sauri yanzu. Wata sanarwar da ta fito daga fadar White House tace Mr. Obama ya bayyana haka ne jiya asabar a tattaunawarshi ta wayar tarho da PM Birtaniya David Cameron, da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da kuma sarkin daular larabawa Mohammed bin Zayed. Kakakin Downing Street, yace Mr. Cameron da Mr. Obama sun amince cewa, Misira na bukatar shata hanya ta zahiri ta gudanar da canji a harkokin siyasar kasar ba tare da bata lokaci ba. Jami’an fadar White House sun ce mataimakin shugaban kasar Joe Biden ya jadada sakon Mr. Obama ga mataimakin shugaban kasar Masar Omar Suleiman ta wayar tarho jiya asabar. Biden ya kuma tambayi Suleiman dangane da ci gaban da ake samu a tattaunawar da ake yi da sauran bangarori domin ganin an biya bukatun mutanen kasar Masar. Fadar White House ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar Masar da ta gabatar da shirin garambawul kwakkwara, da aininin lokacin yin haka, da kuma daukar matakan gaggawa da zasu jadada niyarta ta yin garambawul. Mataimakin shugaban kasar Amurka shima ya bayyana damuwa dangane da sumamen da ake kaiwa al’umma ya kuma yi kira da a saki ‘yan jarida da ‘yan gwaggwarmaya da kuma masu fafatukar kare hakin bil’adama ba tare da bata lokaci ba, wadanda Washington take gani an kama ba gaira ba dalili.

XS
SM
MD
LG