Accessibility links

Shugaba Obama yace babu hujjar kasa cimma matsa kan kudin da kasar zata iya rantowa


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga ‘yan majalisar membobin jam’iyar Republican da Democrat da su cimma matsaya a kan shirin da zai bada izinin kara adadin basusukan da kasar zata iya karba yayinda kasar ke dab da fuskantar gaza biyan basusukan dake kanta.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga ‘yan majalisar membobin jam’iyar Republican da Democrat da su cimma matsaya a kan shirin da zai bada izinin kara adadin basusukan da kasar zata iya karba yayinda kasar ke dab da fuskantar gaza biyan basusukan dake kanta. A cikin jawabin mako mako da aka saba gabatarwar, yau asabar shugaba Obama yace tilas ne bangarorin biyu su cimma daidaito nan da ranar Talata domin Amurka ta iya biyan basukan dake kanta kan lokaci. Bisa ga cewarshi, banbancin dake tsakanin jam’iyun kan batutuwan da ake tankiya a kai ba masu yawa bane, ya kuma bayyana cewa, ba bu hujjar kaza cimma yarjejeniya. Jiya jumma'a majalisar dattijai da jam'iyar Democrat ke rinjaye ta yi watsi da shirin jam'iyar Republican na kara kudin da Amurka zata iya rantowa. Majalisar wakilai ta amince da dokar da kakakin majalisar John Boehner ya gabatar. Shugaba Obama yace shirin na Boehner zai sake dabaibaye tattalin arzikin Amurka da siyasar Washington ta wajen tilasta kasar sake komawa gidan jiya a cikin 'yan watanni kalilan. Shirin ya bukaci a kara yawan bashin da Amurka zata iya rantowa nan da nan da naira biliyan dari tara a kuma rage kudin da gwamnati take kashewa da dala biliyan dari tara cikin shekaru goma masu zuwa. Tare da yin tayin kara yawan kudin da Amurka zata iya rantowa farkon shekara mai zuwa idan za a iya neman hanyar sake rage kudin ta take kashewa. A cikin jawabin jam’iyar Republican na mako mako, Saneta Jon Kyl yace bakin ‘yan jam’iyar Republican ya zo daya cewa, kara yawan bashin da kasar zata iya ci ba tare da gagarumin rage kudin da gwamnati ke kashewa ba wauta ce. shugabannin jam'iyar Democrat a majalisar dattijai sun yi kira ga 'yan jam'iyar Republican a majalisa su goyi bayan shirn shugaban masu rinjaye Harry Reid na rage kudin da gwamnati ke kashewa da dala trillion biyu da biliyan dubu biyu, a kuma kara yawan kudin da Amurka zata iya rantowa da zai ba gwamnati damar ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa karshen shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

XS
SM
MD
LG