Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Maganar Wariya A Bijirewa Taken Amurka - Inji Shugaba Trump


Yan Wasa
Yan Wasa

A yau litinin Shugaban Amurka Donald Trump yace ba abinda ya hada maganar wariyar launin fata da taken kasa da wasu manyan 'yan wasa ke bijirewa yayin da ake buga taken kasa.

Duk da cewar galibin yan wasan sun ce sun yi haka don kalubalantar nuna wariyar launin fata da cin zarafi da yan sanda ke yiwa Amurkawa marasa rinjayi, shugaban ya musunta hakan.

Daruruwar yan wasan da masu horar dasu da ma masu kungiyoyin wasan sun bijerewa shugaba Trump inda suka yi zaman su wasu kuma suka durkusa kana wasu suka tike hannayen juna yayin da ake buga taken kasar domin fara wasanni 14, a maimakon dora hannu a kan kirji yayin da ake taken kasar don nuna goyon baya ga tutar kasar da ma kasar baki daya.

Kalubalantar nuna wariyar launin ya fara ne a bara inda tsohon dan wasan San Francisco Colin Kaepenick dan shekaru 49 a duniya ya durkusa a maimakon mikewa tsaye yayin da ake buga taken kasar don nuna kalubalensa ga yanda yan sanda ke yiwa marasa rinjayi.

Wani karamin adadi na yan wasan hukumar NFL sun dauki durkusawa a matsayin hanyar nuna kalubalanta kafin jiya Lahadi, amma kalubalen na jiya Lahadin yayi kaimi ne biyo bayan sukar da Trump yayi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG