Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Ce Tuntubar Juna Da Rasha Alheri Ne Ga Amurka


Shugaban Rasha Putin da Shugaban Amurka Trump
Shugaban Rasha Putin da Shugaban Amurka Trump

Jiya Talata shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana fatar cewa "zai dasa" da Rasaha, ya furta hakane a lokacinda yake ganawa da shugabannin uku na kasashen da suke yankin Baltic a fadar White House.

Shugaba Trump ya buga-kirci da cewa babu "babu shugaban Amurka da ya fishi tsananta wa Rasha" duk da haka ya dage cewa abunda ake bukata shine karin hanyoyin tuntubar juna da shugaban na Rasha, wanda a ganin Mr. Trump zai kasance alheri ga Amurka.

Sai dai kwararru sun ce da karuwar zaman dar-dar bayan harin guba kan wani tsohon jami'in leken asiri na Rasha mai fuska biyu a Ingila, yanzu ba lokaci ne da ya dace shugaban na Amurka ya gayyaci Mr. Putin zuwa fadar white House ba. Hukumomin Rasha a Moscow sun musanta cewa su suka kai harin guba a kan dan kasarta a Ingila.

A gefe daya,an yanke wa wani lauya dan kasar Dutch dake da zama a Ingila hukuncin daurin wata daya da tarar dala dubu 20, saboda ya shirga wa jami'an lauyan Amurka na musamman dake binciken shishigin da Rasha tayi a zaben shugaban kasar Amurka na 2016 karya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG