Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa a Fadar White House Trump Da Putin Za Su Gana


Shugaba Trump da Shugaba Putin

Ya zuwa yanzu dai babu wani shiri takamaimai da aka fara game da ganawar da ake shirin yi tsakanin Teump da Putin.

Sakatariyar yada labaran fadar shugaban Amurka Sarah Huckabee Sanders ta ce shugaba Donald Trump ya bada shawarar anfani da fadarsa ta White House a matsayin wurin da za a yi ganawa tsakaninsa da shugaban Rasha Vladimir Putin.

Wannan shawarar ta zo ne ranar 20 ga watan Maris a lokacin wata wayar Tarho tsakanin shugabannin biyu. Bayan wayar, Trump ya ce yana fatan ganawa da Putin nan ba da dadewa ba,” amma bangarorin biyu sun ce babu wani shiri da aka fara don ganawar ya zuwa yanzu.

Sanders ba ta dai bada wani karin bayani ba akan shirin ganawar ba.

Shi ma hadimin fadar shugaban Rasha ta Kremlin, Yuri Ushakov ya tabbatar da cewa Trump ne ya fara kawo shawarar ganawar da Putin a fadar White House.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG