Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Gana Da Sarki Abdullah na Jordan


Shugaba Donald Trump ya gana da Sarki Abdullah II na Jordan
Shugaba Donald Trump ya gana da Sarki Abdullah II na Jordan

Shugaban Amurka Donald Trump ya gana Sarki Abdullah na Jordan dangane da tattaunawa tsakanin Isra’ila da yankin Palasdinawa da ta cije. Kawo yanzu, fadar White House bata yi wani Karin haske dangane da matakan wanzar da zaman lafiyan ba.

Yayinda Amurka ke shirin bayyana shirinta na wanzar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, Shugaba Trump yana buga kirji cewa, shirinsa na wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da yankin Palasdinawa, wani shiri ne gagarumi irin da ba a taba gani ba.

Yayin ganawarsa a Fadar White House da Sarki Abdullah, Shugaba Trump bai yiwa manema labarai cikakken bayani a kai ba.

Trump yace "Mai Martaba yasan muna kokari ainun a Gabas Ta Tsakiya, an sami ci gaba sosai a gabas ta tsakiya, ana fara daukar kwararan matakai faro daga soke wannan mummunar yarjejeniyar da Iran. Wannan yarjejeniyar shirme ne kawai, tunda muka soketa, al’amura sun canza ainun".

Nasarar shirin zata ta’alaka ne kan goyon bayan da za a samu daga yanakin, da ya hada da goyon bayan Sarkin Jordan, wanda ya yi kira ga gwamnatin shugaba Trump ta goi bayan kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG