Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Gana Da Shugabannin Kamfanin Jirgin Sama Na Boeing 737-Max 8


Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na dari-dari dangane da kiran da ake yi a cikin gida da kuma kasashen duniya, akan ta dakatar da amfani da jiragen sama, wanda a cikin watanni 6 ya kashe sama da mutane 350.

Shugaba Trump ya gana da shugabannin kamfanin na Boeing 737-Max 8, a cewar ma’aikatan fadar White House duk dai da cewar basu fadi dawa yayi ganawar ba.

Shugaban kamfanin na Boeing Dennis Muilenburg, ya tabbatar ma shugaba Trump ta wayar tarho cewar jiragen suna da nagartar da ta dace, a cewar hukumomin kamfanin.

Fadar ta White House ta tabbatar da wayar tsakanin shugabannin biyu, amma basu fadi yadda tattaunawar ta gudanaba, wadda akayi bayan sukar da Trump yayi a shafinsa na Twitter inda yake cewar “Yanzu tafiya a jirin sama na neman zama abu mai wuya”.

Trump ya kara da cewar ya kamata a saukar da jiragen, har sai an gano musabbabin da yasa suke yin hadari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG