Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Kai Ziyarar Jaje A Birnin Pittsburgh


Uwargida Melania Trump, tare da Shugaba Donald Trump, da limamin Tree of Life Rabbi Jeffrey Myers,

Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump sun kai ziyara a wurin ibadar Yahudawa a Pittsburgh, inda wani dan bindiga ya kashe mutane 11 a ranar Asabar da ta shige yayin da suke ibada

Trump ya gaisa da babban limamin wurin ibadar Jeffery Myers da kuma jakadar Isra’ila a Amurka Rom Dermer.

Shugaba Trump da Melania sun aza dutse a kan kowace kusurwar tambarin Isra’ila na Taurarin Annabi Dawuda wato "Stars of David" a turance a wajen ibadar. Aza dutse a kan kabari ko kan wani wurin tarihi wata tsohuwar al’ada ce ta Yahudawa.

Tarin jama’a masu kalubalantar ziyarar Trump ya kai, sun yi maci a kusa da wurin ibadar. Galibinsu suna ihu suna cewa ku juya bayanku, bisa tsammanin ayarin baburan shugaban kasar zai gabansu a lokacin da shugaban kasar ke kan hanyarsa zuwa asibiti domin ganin wasu ‘yan sanda da suka ji rauni a lokacin harbin.

Masu zanga zangar da wasu ‘yan siyasa da ma wasu shugabannin Yahudawan, sun bukaci shugaban ya yi Allah wadai da masu fifta farar fata a kan kowane jinsi, maimakon ziyarar da ya kai a Pittsburg.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG