Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Yi Barazanar Dakatar Da Ayyukan Gwamnati


Ganawar shugaba Donald Trump da shugabannin majalisar dokokin aMURKA

Shugaban Amurka Donald Trump da shugabannin Democrats a majalisun kasar sun yi sa insa a jiya Talata a kan batun kudin gina katangar kudancin kasar dake iyaka da kasar Mexico, inda Trump yake cewa zai yi alfahari da rufe wasu harkokin gwamnati idan har aka ci gaba da takaddama a kan wannan batu.

Trump ya gayyaci shugabannin marasa rinjayi a majalisun kasar da suka hada da Chuck Schumer na majalisar dattawa da kuma Nancy Pelosi ta majalisar wakilai a kan takaddamar kasafin kudin kasar.

Trump da shugabannin Democrats su biyu sun yi kace nace a kan batun katangar a gaban idon manema labara a ofishin shugaban kasa na Oval office,

Shugaban kasar dan jami’iyar Republican yace an kammala gina wani bangaren katangar kuma zata bada tsaro a kan iyakarmu ainun, amma su ‘yan Democrats din sun musunta wannan batu.

Shugaba Trump ya jadada cewa, zai rufe gwamnati idan basu bashi hadin kai ba

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG