Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Gabatar da Jawabi A Babban Taron Masu Ra'ayin Rikau Yau


Donald Trump, Shugaban Amurka
Donald Trump, Shugaban Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai gabatar da jawabi ga babban taron ‘yan ra’ayin rikau a yau Juma’a a kwanaki uku na karshe da aka kwashe ana gabatar da taron kungiyar Conservative Political Action Conference, wanda ake gabatarwa a wannan shekarar a birnin Washington DC.

Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence yayi jawabi a wajen taron jiya Alhamis, inda yayiwa taron mabiya akidar ra’ayin rikau gwamnatin Shugaba Trump “ Zata cika alkawaruran shugaban yayi lokacin neman zabe.”

Pence shine mai mukami mafi girma daga Jam’iyyar Republican da yayi magana a taron wonda kuma shi ne mafi girma na ‘yan ra’ayin rikau a da akeyi kowace shekara.

Taron akeyi a Maryland Hotel dake National Harbor yana zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar Republican ke rike da majalisun dokokin kasar biyu tare da shugabancin kasar a karon farko cikin shekaru goma.

A jawabinsa da ya kasance kamar kamfen, Pence ya kira maigidansa, Shugaban kasa Trump a matsayin mutum mai jajircewa da kuma hangen nesa da karfin hali” sannnan yace tuni Trump ya fara aiwatar da alkawarurrukan da yayiwa Al’ummar Amurka a yayin da yake Kamfen din neman zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG