Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Allah Wadai Da Masu Yin Barazana Ga Yahudawan Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin ziyararsa a dakin adana kayan tarihin Amurkawa 'Yan asalin Afrika
Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin ziyararsa a dakin adana kayan tarihin Amurkawa 'Yan asalin Afrika

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai da karin sakonnin barazanar da ake aikawa al’umar Yahudawa a duk fadin kasar, wadanda ke nuna cewa ana kyamatar su.

Trump ya yi wadannan kalamai ne a yau Talata yayin wata ziyara da ya kai dakin adana kayan tarihi da al’adu, na kasa na Amurkawa ‘yan asalin Afrika dake nan Washington.

Yayin ziyarar, mutumin da Trump ya zaba a matsayin Sakataren raya birane da samar da gidaje, Ben Carson, ya rufawa shugaban baya, wanda kuma shima- wato Carson, ya ke da kayan tarihi a wurin.

Barazanar da ake wa Yahudawa a cibiyoyinsu abin a yi Allah wadai da shi ne kuma abin takaici ne wanda ke nuni da cewa akwai sauran aiki a gabanmu na ganin mun kawar da nuna kiyayya da banbance-banbance.” In ji Trump.

Wadannan kalamai na shugaba Trump na zuwa ne kwana guda bayan da wata kungiya mai yaki da matsalar nuna wariya ta ruwaito cewa akalla cibiyoyin Yahudawa 10 a wasu jihohin Amurka suka samu wasikar dake cewa za a kai masu harin bam.

A kuma lokacin ziyarar da yake yi a dakin adana kayan tarihin na Amurka ‘yan asalin Afrika, Trump ya karanto sunayen fitattun bakaken fata Amurkawa da suka taimaka wajen yiwa kasa hidima.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG