Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Zabi Mace a Matsayin Alkali a Kotun Koli


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai gabatar da mace wadda za ta zama Alkali a babbar Kotun Kolin Amurka, biyo bayan mutuwar mai shari’a Ruth Bader Ginsburg.

“Zan gabatar da dan takara a mako mai zuwa. Za ta zama mace,” Trump ya fada a wurin gangamin siyasa a garin Fayetterville, dake jihar North Carolina. ya ci gaba da cewa “Ina tunanin kamata ya yi ta zama mace, saboda ina son mata sosai sama da maza.”

Yayin da Trump ke magana, magoya bayansa suka rera waka suna cewa, “Cika wannan gurbin.”

Tun farko dai, ya yabawa wasu mata biyu a matsayin zabinsa na Alkalin Kotun Koli.

An sassauta tutar Amurka a babbar Kotun Koli bayan rasuwar Gainsburg
An sassauta tutar Amurka a babbar Kotun Koli bayan rasuwar Gainsburg

Rasuwar Ginsburga ranar Juma’a sakamakon cutar Sankara bayan kwashe shekaru 27 a Kotun ya baiwa Trump dama, wanda ke fuskantar sake tsayawa takara ranar 3 ga watan Nuwamba, wannan damar ta baiwa masu ra’ayin mazan jiya zama masu rinjaye da 6-3.

Duk wanda aka zaba sai Majalisar Dattawa ta amince, inda jam’iyyar Trump ta Republican ke da rinjaye a Majalisar da 53-47.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG