Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Xi Jinping Ya Samu Shugabancin Jam'iyyar Kwaminis Wa'adi Na Biyu


A hukumance an sanarda sake zaben shugaban kasar China XI Jinping wa’adi na biyu, a matsayin shugaban jam’iyyar kwamunis yau Laraba.

Shugaban kasar China, mai shekaru 64 da haihuwa ya tsaya tare da sabbin mambobin kwamitin zartarwar kasar su biyar a zauren ginin majalissar kasar dake Beijing, bayan da kwamitin dake kula da harkokin jam’iyyar kwamunis ya zabe su.

Cikin sabbin mambobin kwamitin harda Zhao Leji, wanda ya karbi jagorancin kwamitin dake kula da harkoki, da ladabtarwar jam’iyyar daga hannun Mr. Wang Qishan, wanda ya jagoranci shirin yaki da cin hanci da rashawar shugaba Xi Jinping.

Mamba daya tak da ya dawo daga kwamitin zartaswar jam’iyyar mai mulki tare da shugaba Xi shine firimiya Li Keqiang, dan shekaru 62 da haihuwa.

Sauran mambobin suma cikin shekarun su na sittin da haihuwa, hakan ya bar jam’iyyar ba tare da wani da zai gaji gurbin shugaba Xi Jinping ba idan wa’adinsa ya kare a shekarar 2022, Kwararru sun ce kasancewar babu wani magaji a jam’iyyar na nuna cewa ta yiwu shugaba Xi ya kara zarcewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG