Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Philippines Na Shirin Tado Da Batun Tekun Kudancin China A Taron APEC.


Shugaba Rodrigo Duterte yace yana da tambayoyin da zai yiwa Beijing a taron kungiyar kasashen yankin Asiya.

A halin da ake ciki kuma, shugaba Rodrigo Duterte yace yana da niyyar tambayar Beijing a yayin taron kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pacific da ake kira APEC a takaice, ko menene shirin kasar a kan tekun kudancin China, kuma ko za a kyale kasashen da suke kudu maso gabashin Asiya su yi zirga-zirga a tekun ba tare da tsangwama ba.

A cikin kusan watanni goma sha takwas da ya yi bisa karagar mulki, Duterte ya dauki salon lalama a dangantakarsa da Beijing da kuma batun ikirarinta na mallakar tekun kudancin China.

Kakakin shugaban kasar Ernesto Abella, ya bayyana a cikin watan Oktoba na shekara ta dubu biyu da goma sha shida cewa, sa’in-sa ba zai taimaki kasar Philippines ba, dalili ke nan da ya sa Duterte ya gwammace daukar matakin tattaunawar da zata tabbatar da kare mutuncin Manila.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG