Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Bayyana Shirin Ruguza Kungiyar ISIS


Shugaba Barack Obama yayinda yake yiwa kasar jawabi daga fadarsa a Washington, jiya Sept. 10, 2014.

Yanzu ta bayyana fili cewa Amurka ta shirya ta kai hari akan kungiyar ISIS a inda ta kafa hedkwarta cikin kasar Syria da nufin ruguza kungiya gaba daya.

Karon farko Shugaban Amurka Barack Obama ya bada umarnin yiwuwar kai hari da jiragen sama kan mayakan ISIS a Syria.

Da yake bayyana shirinsa na tunkarar mayakan jiya Laraba, Mr Obama yace Amurka zata jagoranci wannan yunkurin babu kakkautawa domin kawar da mayakan ISIS masu tsatsauran ra’ayi a duk inda suke ta wajen amfani da karfin da take da shi ta kai hari a sararin sama da kuma hadin kan da zata samu daga dakarun hadin gwuiwa.

Yace wannan ba fadan mu ba ne mu kadai, Amerika zata iya amfani da karfinta wajen taka rawar gani, amma ba zamu yiwa al’ummar Iraqi abinda ya kamata su yiwa kansu ba, ba kuma zamu maye gurbin abokan kawancenmu Labarawa wajen samar da tsaro a yankinsu. Dalili ke nan da ya sa aka jajirce cewa karin matakin da Amurka zata dauka ya danganta ga kafa gwamnatin da zata ba kowa dama a Iraqi, abinda aka yi kwanan nan.

Shugaba Obama ya bayyana cewa, manufar Amurka a fili take karara, ta rage karfin kungiyar mayakan daga baya kuma a ruguza ta kwata kwata ta wajen aiwatar da gawurtaccen tsarin yaki da ta’addanci.

Yace bari in yi bayani kan wadansu abu biyu, akidar kungiyar ISIL ba musulunci bane. Babu addinin da ya lamunci kashe mutanen da basu ci ba basu sha ba, kuma galibin wadanda kungiyar ISIL ta kashe Musulmi ne. Kungiya ce da take da alaka da al-Qaida a da, wadda ta fake da rikicin bangarancin da ake yi da kuma yakin basasa a Syria ta kwace wadansu sassa dake kan iyakar Iraqi da Syria. Bata da goyon bayan gwamnati ko kuma mutanen da take gallazawa. Kungiyar ISIL kungiyar ta’addanci ce, illa iyaka. Bata da wata manufa sai yiwa duk wadanda suka yi tsayayya da ita yankan rago.

Shugaba Obama ya bayyana matakai hudu da Amurka zata dauka da suka hada da ci gaba da kai harin sararin sama da aka fara samun nasarar korar mayakan daga cikin Iraqi. Wannan na nufin kai hari cikin Syria karon farko idan ta kama.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG