Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Dawo Gida Bakin Aiki


Shugaban Amurka ya dawo ga rayuwa da ya saba da ita a Washington jiya Lahadi, inda yake suka ga rahotannin da suka danganci hargitsin fadar White House da binciken da ake yiwa jami’ansa da huldansu da Rasha.

A ranarsa ta farko bayan bulaguro da yayi na kwanaki tara a Gabas ta Tsakiya da Turai, Trump ya fada a sakon Twitter cewar bulaguron nasa babban Alheri ne ga Amurka. Yace babban aiki ne mai kyakkyawar sakamako.


Sai dai nan da nan ya maida hankali ga bayyana damuwarsa ga kafofin yada labarai da ya dade yana yi.


Trump yace shi a ra’ayinsa, bayanai da ake kwarmatawa daga fadar White House karya ce, wasu kafofin yada labarai na jabu ne suka kirkirowa.

Yace a duk lokacin da kafafen labaran karyar suka ce wata majiya tace ba tare da bayyana suna ba, to lallai ne babu wannan majiyar, amma sai mawallafan labaran karyar su kirkiri. Yace kafafen labarai na jabu abokan gaba ne.


Shugaba Trump da jami’ansa suna huskantar bincike na tsawon watanni a kan alakarsu da jami’an kasar Rasha a lokacin yakin neman zabe da ma bayan haka.

Akwai kuma wasu zargi da jami’iyar adawa ta Democrat take yi cewar Trump ya yi yunkuri yin katsalanda a harkar shari’a da kuma bincike.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG