Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Zargi Kotuna da Yin Siyasa


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya gaya ma manyan jami'in tsaro cewa, siyasa ce ta sa kotuna su ka dakatar da ikon Zartaswa da ya yi amfani da shi kan batun shigowar baki, sannan ya yi gargadin cewa babu tabbas kan yanayin tsaron kasa, muddun ba’a tsaurara sharuddan shigowa kasar ba.

"Mu na cikin hadari saboda abin da ya faru," a cewar Trump a taron da yayi da kungiyar Manyan Jami'an Tsaro na Manyan Birane a Washington fadar gwamnatin Amurka.

"Ban taba son in kira wata kotu mara adalci ba, don haka ba zan kira wannan kotun mara adalci ba," a cewar Trump. Duk da yake har yanzu kotun ba ta yanke shawara kan batun ba, Trump ya ce "da alamar kotunan na siyasa ainun. Idan da za su iya nazarin takardar sannan su yi abin da ya dace, zai taimaki bangaren shari'a sosai."

Wata kotun daukaka kara da ke San Francisco ta ce mai yiwuwa ta yanke hukunci kan ko shin alkalin kotun tarayya na da hurumin dakatar da umurnin hana shigowar mutane daga wasu kasashe 7 masu rinjayen Musulmi.

XS
SM
MD
LG