Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Trump Da Uwargidansa Sun Kamu Da Coronavirus


Shugaban Amurka Donald Trump da Uwargidansa Melania Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da asubahin yau Jumma'a cewa shi da Uwargidansa Malania sun kama cutar Coronavirus

Shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa sun "fara killace kansu" bayanda daya daga cikin hadimansa ta kurkusa Hope Hicks wadda ta yi ta tafiye-tafiye da shi a makonnin nan a cikin jirgin shugaban kasa, ta kamu da cutar.

Shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na twitter yau jumma'a da asuba cewa, " A daren nan Uwargidan shugaban kasa da ni mun kamu da cutar COVID-19," "Zamu fara killace kanmu da kuma neman lafiya ba tare da bata lokaci ba. Zamu fuskanci wannan TARE!"

A cikin sanarwar da likitan Fadar Shugaban kasa Sean Conley ya fitar, ya ce yana sa ran shugaban kasar zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba.

Sanarwar ta shugaba Trump ta zo ne 'yan sa'oi bayan da rahotannin suka bulla cewa daya daga cikin hadiman Fadar White House Hope Hicks ta kamu da cutar Coronavirus.

Hope Hicks
Hope Hicks

Tun kafin sanar da sakamakon gwajin cutar, Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa shi da Uwargidansa sun fara killace kansu yayinda ya kuma sanar cewa mataimakiyarsa Hope Hicks ta kamu da cutar.

Ya ce "Hope Hicks, wadda take aiki tukuru ba tare da hutu ba ko na karamin lokaci, ta kamu da cutar Covid 19. Abin ba dadi! Ni da Uwargida muna jiran sakamakon gwajin. Kafin nan, mun fara daukar matakin killace kanmu!

Trump shi ne shugaban kasashen duniya na baya bayan nan da ya kamu da cutar. A watan Maris Firai Ministan Birtaniya Borris Johnshon ya zama shugaban kasa na farko da ya kamu da cutar, kafin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya biyo baya a watan Yuli, ya kuma yi gwaji a lokuta da dama inda aka yi ta samunshi da kwayar cutar, sai dai dukan shugabannnin biyu sun murmure.

Kawo yanzu, sama da mutane dubu dari biyu suka mutu da cutar CODVID-19 a Amurka, yayinda sama da mutane miliyan shida kuma suka kamu da cutar a kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG