Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wai Obama Musulmi Ne?


Amurkawa da yawa na yi wa shugaban kasarsu, Barack Obama, daukan cewa shi Musulmi ne, duk kuwa da musantawar da ya sha yi, na cewa shi, Kirista ne.

Wasu bincike-binceken jin ra’ayoyin jama’a har aji biyu da aka gudanar sun nuna cewa kowane mutum daya daga cikin Amurkawa biyar yana yi wa shugaba Barack Obama daukan cewa shi Musulmi ne – duk kuwa da sanin cewa Obama Kirista ne, da kuma nanatawar da ya sha yi, cewa shi fa Kirista ne. Binciken ra’ayin jama’a da mujallar Time ta yi, ya nuna cewa 24% na Amurkawa duk suna yi wa shugaba Obama daukan Musulmi, wanda wannan ya banbanta da binciken da cibiyar Pew Research Center ta gudanar, don ita kashi 18% na Amurkawa ta gano masu irin wannan ra’ayin. Jiya ma sai dai wani kakakin fadar White House wai shi Bill Burton ya sake nanata cewa shugaba Obama Kirista ne dake zuwa wajen adduoi kullum. Binciken na cibiyar Pew din har ila yau ya nuna cewa mutasnen dake wa Obama kallon cewa shi Musulmi ne, suna nuna rashin gamsuwa da yadda yake gudanarda aikinsa na shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG