Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Amince Ya Gana Da Shugaban Koriya ta Arewa


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump

Sanadiyar gayyatar da shugaban Koriya ta Arewa ya yiwa Shugaban Amurka Donald Trump, yanzu shugabannin biyu zasu gana a watan Mayu mai zuwa da nufin kawo karshen takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu biyo bayan barazanar da Amurka ta ce Koriyan na yiwa zaman lafiyar duniya

Fadar White House ta ce shugaba Donald Trump ya amince da gayyatar tattaunawa da Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa yayi masa, amma duk da haka, za a ci gaba da yin aiki da dukkan matakan takunkumin da aka sanya ma kasar.

Shugaba Kim ya bayyana aniyar ganawa da shugaba Trump, ta hannun Chung Eui-yong, mai ba shugaban Koriya ta Kudu shawara kan harkokin tsaron kasa, wanda yayi tattaki zuwa Koriya ta Arewa kwanakin baya.

Chung ya bayyana wannan matakin mai dimbin tarihi da ban mamaki cikin daren nan na alhamis agogon Washington, a kofar fadar White House.

Jim kadan da bayyana wannan sako ne sai shugaba Trump ya bayyana shi a shafinsa na twiter.

Abinda ko yake cewa, shine ‘’Kim Jong Un yayi maganar kawar da makaman nukiliya tare da wakilin Koriya ta Kudu. Haka kuma Koriya ta Arewa ba zata yi gwajin makamai masu linzami a wannan lokacin ba. Ba shakka an fara samun gagarumin ci gaba."

Mai Magana da yawun fadar ta White House Sarah Sander Hukabee ita ma ta fada a shafin ta na twitter cewa shugaba Trump da Kim zasu gana a wani lokaci kuma a wani wurin da za'a sanar nan gaba.

Sai dai Sanders tace "muna fatar ganin tabbatar batun kawar da makaman nukiliya daga Koriya ta Arewa. Amma kuma, tilas a ci gaba da yin aiki da dukkan matakan takunkumi da matsin lamba a kan kasar."

Chung ya bayyana na wani dan takaitaccen lokaci a kofar fadar White House jiya alhamis domin sanar da cewa Kim ya kosa da ya hadu da shugaba Trump ba tare da bata lokaci ba. Har ila yau yace Kim ya kuduri aniyar dakatar da gwaje-gwajen nukiliya da makamai masu linzami.

Chung yace shugaba Trump ya fada masa cewa yana son ganawa da shugaba Kim nan da watan Mayu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG