Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce a shirye Yake Ya Dauki Tsauraran Matakai Kan Koriya ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka ya ce zai iya daukan tsauraran matakai akan Koriya ta Arewa amma yana fatan ba zasu tabbata ba biyo bayan labarin dake cewa Koriya ta Arewa ta nuna alamar son tattaunawa da Amurka akn shirin nukiliyarta

Shugaba Donald Trump yace a shirye Amurka take ta dauki tsatsauran mataki dangane da kokarin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami da za a iya dana musu kundojin nukiliya, amma kuma ya ce yana fata "matakin zai zamo wanda ya dace."

Kalaman shugaban sun biyo bayan sanarwar da Koriya ta Kudu ta fitar jiya Talata cewa, Koriya ta Arewa ta nuna cewa a shirye take ta fara tattaunawa da Amurka a kan dakatar da shirin makaman nukiliyarta.

Kalaman Trump na baya bayan nan a kan Koriya ta Arewa, sun sha bamban da irin barazanar da ya yi a baya, cewa Pyongyang zata huskanci wuta da fushi idan ta ci gaba da kera makaman kare dangi


Wani babban jami’in gwamnatin Amurka yace ra;ayin gwamnatin Trump a bude yake, amma kuma tana dari-dari da manufofi ko aniyar Pyongyang, yana mai cewa a cikin shekaru 27 da suka wuce, Koriya ta ARewa ta yi kaurin suna wajen "karya duk wani alkawari ko yarjejeniyar da ta kulla da Amurka da sauran kasashen duniya."

Jami’in, wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya kara da cewa, "yana da kyau kowa yayi la'akari da wannan, a kuma sanya ido a ga abinda zai faru."

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG