Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Dorawa OPEC Alhakin Tashin Farashin Mai


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi OPEC, kungiyar kasashe 14 masu sayar da mai da haddasa tashin farashin man a kasuwar duniya daga dala 30 zuwa dala 70 cikin shekara daya lamarin d aya ce bashi da kyau

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce farashin mai ya yi tashin goron zabi, yana mai dora alhakin hakan akan OPEC, kungiyar kasashen da ke da arzikin man.

A jiya Laraba Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa “farashin mai ya tashi sosai, OPEC ta yi halinta, hakan babu kyau.”

Kungiyar ta OPEC mai mambobi 14 da suka hada har da Saudiyya, Iran, Iraqi, Kuwait da Venezuela, kan samar da kashi 40 na man da ake hakowa a duniya, wanda kusan kashi 60 cikin 100 na adadin wannan man akan sayar da shi ne a kasuwannin duniya.

A duk lokacin da kungiyar ta OPEC ta yanke shawarar kara adadin man da ake hakowa ko kuma akasin hakan, matakin kan shafi farashin mai a duniya, lamarin da ke shafar masu amfani da man da kuma hadahadar kasuwancinsa.

A shekarar 2016 ne, shugabannin kungiyar ta OPEC suka cimma wata matsaya ta rage adadin man da ake hakowa zuwa ganga miliyan 1.8 a kowacce rana, domin a rage kwantan da yake yi a kasuwanni.

Tun kuma daga lokacin ne farashin man ya tashi daga kasa da dala 30 kan kowacce ganga zuwa sama dala 70.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG