Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Hakikance Kan Janye Sojojin Kasar Daga Syria


Shugaban Amurka, Donald Trump speaks
Shugaban Amurka, Donald Trump speaks

Duk da shawarar da kwararru ke bashi cewa ISIS na iya komawa Syria tare da fargaban kawayen kasar, shugaban Amurka ya hakikance sai ya janye sojojin kasarsa daga Syria

Gameda batun soji har yanzu, shugaban Amurka Donald Trump, yana nan kan bakarsa kan ikirarin da yayi cewa, lokaci yayi na janye sojojin Amurka daga Syria, duk da cewa kawayen Amurka da suke kasar suna kiran da ta sake tunani.

"Babban burin mu na zuwa can shine ganin mun kawar da ISIS, Mr. Trump ya fada jiya talata. "kusan mun kammala wannan aiki, kuma zamu yanke shawara nan ba da jumawa ba tareda shawara da wadansu, kan abunda zamu yi," shugaban na Amurka ya fada a wani taro da manema labarai da ya yi tareda shugabannin kasashen yankin Baltic su uku.

Sai dai wannan matakin janye sojojin Amurkan kawayen Amurka basu goyi bayan haka, ciki ko harda kasar Iraqi da Kurdawa.

Da dama suna fargabar hakan zai bar gibi da wasu ciki harda ISIS zasu cike shi.

Ahalinda ake ciki kuma, wata mata ta bude wuta a helkwatar kamfanin Youtube a jahar California ta jikkata kanta da mutum uku kamin ta kashe kanta, kamar yadda hukumomi a yankin suka yi bayani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG