Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashin Da Ya Kai Hare Haren Bama-Bamai A Jihar Texas Ya Kashe Kansa


Shugaban ‘yan sanda na yankin Austin dake jihar Texas a nan Amurka, Brian Manley yace mutumen da ake zargi da kai hare haren bama-bamai Mark Conditt ya bar bidiyo na wani sako mai tsawon mintoci 25 da ya dauka da wayarsa ta hanu kafin ya hallaka kansa.

Hukumomi sun yi gargadin cewa watakila har yanzu akwai sauran bamabaman da basu riga sun tashi ba a garin na Austin, amma a yammacin ranar Laraba sun amincice cewa babu raguwar kunshin bam din da ka iya zama barazana ga jama’ar gari.

‘Yan sanda sun imanin cewa Conditt shine ne mutumin da ya kai hare-hare shidda da bama-bammai a cikin garin Austin da kewaye a sati uku da suka gabata, inda biyar daga ciki suka fashe kuma suka yi sanadiyuar mutuwar mutane biyu da raunata wasu su biyar.

Conditt ya kashe kansa ne yayinda ya saki bam na bakawai a cikin motar sa da safiyar jiya Laraba lokacin da ‘yan sanda suka je kamashi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG