Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban APC Na Jihar Gombe Ya Tsallake Rijiya da Baya


APC

Group Captain Bala Jibrin mai ritaya shugaban APC na wucin gadi a jihar Gombe ya sha da kyar yayinda suke bukin murnar kammala zaben fidda gwani na jihar

A zantawar da yayi da Muryar Amurka Group Captain Bala Jibrin mai ritaya yace sun kammala zaben fidda gwani suna bikin murna sai wasu matasa ukku suka far masa da zage-zage

Matasan basu tsaya nan ba sai da suka cire hularsa suka kai masa duka da kulki kafin jami'an tsaro su shawo kansu su kuma yi awan gaba dasu. Amma kuma sai da suka yi masa barazanar kasheshi

Inji Captain Jibril wadanda suka kai masa hari wai 'yan gidan Sanata Haruna Danjuma Goje ne tsohon gwamnan jihar.

Amma wani na hannun daman Sanata Danjuma Goje Alhaji Garba Tela Wazirin Gombe yace baki shi ke yanka yuwa. Injishi Group Captain Bala Jibrin yana wasu kalamun batanci wa Danjuma Goje lamarin da ya harzuka magoya bayan shi Danjuma Goje. Yace Sanata Goje nada magoya baya da yawa a Gombe saboda haka dole ne yaransa su tashi idan ana zaginsa.

Ana zargin shi Group Captain Bala Jibrin da cewa Sanata Goje ne umalubaisan rikicin jam'iyyar APC a Gombe.

Su yaran 'yansanda sun cafkesu kuma ana shirin gurfanar dasu a kotu.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG