WASHINGTON, DC —
A yau da la’asariyya jagoran ‘yan adawa a jamhuriyyar Nijar, shugaban jam’iyyar Moden Lumana Afirka Hama Amadou, ya koma kasar Nijar bayan kwashe shekaru kusan 5 yana gudun hijira a kasashen waje.
Magoya bayan tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Hama Amadou, sun kece da murna lokacin da ya iso kofar gidansa a birnin Yamai.
Daga saukar sa daga jirgi kai tsaye jagoran ‘yan adawan ya samu yiwa mahaifiyarsa addu’o'i wacce Allah ya yiwa rasuwa a watan Oktoba da ya gabata.
Ga rahoto cikin sauti daga wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 18, 2021
'Yan Adawa A Uganda Sun Ki Yarda Da Sakamakon Zaben Ranar Lahadi
-
Janairu 17, 2021
Shugaba Yoweri Museveni Ya Lashe Zaben Uganda A Karo Na Shida
-
Janairu 12, 2021
Jam'iyyun Adawa Na Kalubalantar Zaben Shugaban Kasar Nijar
-
Janairu 11, 2021
Chadi Za Ta Hada Kai Da Najeriya Wajen Yaki Da 'Yan Boko Haram
Facebook Forum