Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jami’ar ABU Zariya Ya Shaida Dino Melaye A Gaban Majalisar Dattawa


Mataimakin Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello da Ke Zaria, Farfesa Ibrahim Garba, ya bayyana a gaban Kwamitin kare hakki da Ka'idoji na majalisar dattawa inda ya bada shaida cewa dan majalisar dattawa mai wakiltar Jihar Kogi ta Yamma Dino Melaye, ya kammala karatunsa a jami'ar.

Da yake bada shaidar a gaban kwamitin, shugaban jami’ar ya tabbatarwa da majalisar dattawan cewa Dino Melaye, ya kammala karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake karamar hukumar Zariya, ta jihar Kaduna.

Ya kuma kara da cewa bayanan da jami’ar keda su sun bayyana cewa da yake karatu a jami’ar, dan majalisar ya yi amfani da suna Daniel Melaye, wanda daga bisani ya canza zuwa Dino Melaye, ya kammala karatunsa a shekara ta dubu biyu, kuma ya sami digiri mai daraja ta uku (3rd Class) a fannin kimiyyar ilimin taswirar kasa da sararin samaniya (Geography).

A lokacin zaman, majalisar ta bukaci dan majalisar ya kare kansa inda yayi bayanin cewa yana alfahari da jami’ar Ahmadu Bello, kuma har yanzu shi dalibi ne a jami’ar.

Da yake zantawa da wakiliyar sashen Hausa na muryarAmurka, Medina Dauda, Melaye ya bayyana cewa yayi farin cikin shaidar da shugaban jami’ar ya bayar a kansa, ya kuma kara da cewa sharrin mahassada ne kawai, a sakamakon fadar gaskiya komai dacinta da yake yi a majalisar, dan haka ya ce babu shakka zai ci gaba da fadar gaskiya komai dacinta a majalisa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG