Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Kamaru Poul Biya Ya Fara Ziyarar Aiki A Najeriya


Shugabannin Najeriya da Kamaru

Dazu dazunnan ne shugaban kasar Kamaru Poul Biya, ya sauka a babban birnin Najeriya Abuja, domin fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a makwabciyar kasar.

Matsalar Boko Haram na daga cikin batutuwan da shugabannin biyu zasu tatttauna da tsatstsauran ra’ayin dake haddasa ayyukan ta’addanci. Haka kuma shugabannin zasu saka hannun kan wata yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar, ta tabbatar da gayyatar shugaban kamaru Poul Biya da shugaba Mohammadu Buhari yayi.

A shekarar data gabata shugaba Buhari yaje kasar Kamaru, inda ya tattauna da shugaba Poul Biya kan hanyoyin da zasu bi domin dakile ta’addancin kungiyar Boko Haram. Najeriya da Kamaru da Nijar baki daya kasashen sun hada gwiwa wajen yakar Boko Haram.

XS
SM
MD
LG