Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yi Sammacin Gwamnan Jihar Imo Game Da Halin Tsaro a Jihar.


Shugaba Buhari, hagu, da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo (Instagram/Hope Uzodinma)
Shugaba Buhari, hagu, da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo (Instagram/Hope Uzodinma)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, da ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, da babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami, zuwa wani taro a fadar shugaban kasa a yau Litinin.

Shugaban kasar zai gana a lokuta daban-daban da su inda zai nemi karin haske kan al’amuran jihar Imo da bangaren wutar lantarki da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Idan ba a manta ba, shugaban kasar a lokacin da yake yin Allah wadai da tashe-tashen hankula a jihar ta Imo biyo bayan lalata gine-ginen ofishin ‘yan sanda da gidan Farfesa George Obiozor, da kuma shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, ya yi alkawarin sake duba harkokin tsaro da halin da ake ciki a kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana damuwarsa kan matsalar wutar lantarki da ake yawan samu, inda ya nemi gafarar ‘yan Najeriya tare da bada tabbacin samun sauki cikin gaggawa.

XS
SM
MD
LG