Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasa Tinubu Ya Bukaci Hukumomi Da Su Yi Musayar Bayanan Sirri A Tsakaninsu Domin Yaki Da Ta'addanci


Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)
Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)

A ranar Litinin ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dora wa jami’an tsaro da na leken asiri a kasar nan muhimmancin musayar bayanai da bayanan sirri a tsakaninsu, inda ya ce boye irin wadannan bayanai na iya kawo cikas wajen yaki da ta’addanci.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne bayan wata ziyarar aiki da ya kai sabon ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da gine gine a Cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC), da ke Abuja.

Yayin da yake lura da kokarin da aka nuna wajen yakar ta’addanci da kuma na’urorin zamani a cibiyoyin biyu, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fahimci cewa, idan har za a samu farfado da tattalin arziki, da wadata, da ci gaba, ya kamata a ba da fifiko ga tsaro.

Jami'an Tsaro
Jami'an Tsaro

“Abin farin ciki ne sosai ganin cewa muna samun kayan aikin da za mu shirya kanmu.

“Ba Najeriya ce kadai ke fama da ta’addanci ba, duk fadin duniya ne kuma dole ne mu yake shi, dole ne mu kawar da shi gaba daya.

“Idan a matsayinmu na ‘yan Najeriya muna neman farfado da tattalin arziki, wadata da ci gaba, to dole ne mu ba batun tsaro fifiko.

Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)
Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)

“Dole ne a hada karfi da karfe a wannan kasa baki daya ta yadda za a mai da hankali waje daya don tabbatar da tsaron kasar nan.

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana rangadin da ya yi a sabon ginin ONSA a matsayin mai matukar muhimmanci, ya kuma bayyana aniyarsa ta yin duk abin da ya dace don tallafa wa cibiyoyin tsaro na kasa.

A nasa jawabin, NSA, Manjo-Janar Babagana Monguno (Rtd), ya yi alkawarin cewa ONSA za ta jajirce tare da sadaukarwar wajen ganin shugaba Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa al’ummar Najeriya kan tsaro.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG